Close Menu
    Facebook X (Twitter) Instagram
    KADA TIMESKADA TIMES
    • Home
    • News
    • Energy
    • Entertainment
    • Health
    • Politics
    • Religion
    • Sports
    • More
      • Business
      • Education
      • Environment
      • Opinion
      • Security
      • Traditional/tourism
    Subscribe
    KADA TIMESKADA TIMES
    Home » Hukumar Aikin Hajji ta kasa wato NAHCON , Ta Gargadi Maniyata su guji muamala da Yan Damfara Da Sunan Samun Gurbin Hajjin 2027
    News

    Hukumar Aikin Hajji ta kasa wato NAHCON , Ta Gargadi Maniyata su guji muamala da Yan Damfara Da Sunan Samun Gurbin Hajjin 2027

    Malam Mujitaba RamalanBy Malam Mujitaba RamalanAugust 16, 20262 Mins Read
    FB IMG 1786910718517
    FB IMG 1786910718517

    Daga Aliyu Samba

    Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) ta yi gargaɗi ga maniyyatan Hajji da masu gudanar da aikin Hajji na kamfanoni da su yi watsi da duk wani buƙatar kuɗi da wasu mutane za su yi da sunan tabbatar musu da gurbi na musamman a aikin Hajjin shekarar 2027.    

    Read also: Emir of Zazzau Seeks Sustained Efficiency in Hajj Administration*

    Kafar Sadarwar Sabuwar Nigeria ta ce a cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar a Abuja, NAHCON ta ce rabon guraben Hajji yana gudana ne bisa tsarin da aka amince da shi, da kuma ƙa’idojin da hukumar ta gindaya wajen bayar da lasisin kamfanonin da ke shirya Hajji.    

    Hukumar ta ce wasu mutane Yan damfara da ke ikirarin cewa jami’ai ko wakilan NAHCON ne suna kiran kamfanonin shirya Hajji da maniyyata, suna neman kuɗaɗe da sunan tabbatar musu da guraben Hajji na musamman.   

    NAHCON ta bayyana cewa babu wani mutum, wakili, kamfanin shirya Hajji ko wata ƙungiya da aka ba izinin neman ko karɓar wani ƙarin kuɗi ko kuɗin gudanarwa daga maniyyata ko masu shirya Hajji da sunan tabbatar da gurbin Hajjin 2027.   

    Read also: 2027 Budget to Upgrade Agric Training Centre, Enrol 1,000 Youths — Governor Radda

    Hukumar ta ce duk wanda ya tuntubi maniyyaci ko kamfanin shirya Hajji yana neman kuɗi da irin wannan alkawari, yana aikata zamba ne kuma ba shi da wani izini daga hukumar.   

    NAHCON ta buƙaci duk wanda aka yi wa irin wannan da ya kai rahoto ga ‘yan sanda ko wasu hukumomin da ke da alhakin yaƙi da laifuka.    

    Hukumar ta kuma shawarci maniyyatan da su biya kuɗaɗen da aka sanar a hukumance kawai, ta hannun Hukumomin Jin Daɗin Alhazai na Jihohi, bankunan da aka amince da su a ƙarƙashin tsarin adashin Gata,wato Hajj Savings Scheme, ko kuma kamfanonin shirya Hajji da ke da ingantaccen lasisi.

    Read also: Independence Day: Gov. Yusuf Urges Kano Residents to Shun Violence Ahead of 2027 Elections

    NAHCON ta tunatar da maniyyata cewa rashin kammala shigar da bayanan maniyyata kafin ranar 26 ga Satumba 2026, da kuma rashin kammala tura kuɗaɗen Hajji zuwa ranar 2 ga Disamba 2026, na iya haifar da rasa guraben da aka ware, ba tare da la’akari da duk wani alkawari da mutanen da ba su da izini suka yi ba.   

    Hukumar ta ce tana da ƙudurin tabbatar da gudanar da aikin Hajjin 2027 cikin gaskiya, adalci da tsari, tare da kira ga jama’a da su dogara da bayanan da hukumar ke fitarwa ta kafafen sadarwarta na hukuma kawai.

    damfara hajji nahcon Yan
    Share. Facebook Twitter WhatsApp LinkedIn Email Telegram Copy Link
    Previous ArticleKebbi Governor Picks Ibrahim Augie as Running Mate for 2027
    Next Article Governor Yusuf condoles Sheikh Ibrahim Saleh over wife’s death

    Related Posts

    News

    Just In: Nigeria Secures Additional 10,000 Hajj Slots for 2027.

    October 1, 2026
    News

    Nigeria @ 66: Zulum visits hospital, says most kidney failure linked to BP, Diabetes

    October 1, 2026
    News

    Governor Radda Condoles Family of Late Alhaji Sa’adu Kaita Maigishiri

    October 1, 2026
    Add A Comment
    Leave A Reply Cancel Reply

    Latest Posts

    Governor Radda Extols Tinubu as Four Katsina Sons Clinch Federal Appointments

    April 2, 2026314 Views

    Retired Police Officers Plan “Do-or-Die” Peaceful Protest at Villa April 20

    April 5, 2026252 Views

    Emir of Katsina Approves Turbanning of Three Illustrious Sons

    April 1, 2026237 Views

    Saulawa Assumes Office as Acting Customs Provost Marshal, Promises Fair Enforcement of Discipline

    April 25, 2026178 Views

    GENERAL BABANGIDA APPLAUDS AFCSC INITIATIVE, URGES DEEPER COMMUNITY ENGAGEMENT FOR SECURITY

    May 12, 2026173 Views

    FORMER CHAIRMAN MHWUN KATSINA STATE, COMRADE MANNIR, APPEALED TO THE STATE GOVERNMENT TO FULFILLED PROMISE OF PAYING RETIRED WORKERS IN LOCAL GOVERNMENTS.

    May 12, 2026163 Views
    Stay In Touch
    • Facebook
    • YouTube
    • TikTok
    • WhatsApp
    • Twitter
    • Instagram
    © 2026 Kada Times. | Developed by ENGRMKS & CO..
    • Home
    • About Us
    • Advertise With Us
    • Privacy Policy
    • Contact Us

    Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.