Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jamaa,Alhaji Mohammed Idris, ya bukaci ‘yan Nijeriya da su ɗaukaka tunanin su sama da bambance-bambancen addini, ƙabila da siyasa, su haɗa kai wajen yaƙi da rashin tsaro da sauran ƙalubalen da ke fuskantar ƙasar nan.
Idris ya yi wannan horon ne a ranar Talata, a wajen taron ƙasa da ƙasa mai taken “Bambance-bambance da Zaman Lafiyar Al’umma: Haɗin Gwiwa don Kyakkyawar Makoma,” wanda ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatus Sunnah (JIBWIS) ta shirya tare da haɗin gwiwar Ƙungiyar Ƙasashen Musulmi ta Duniya (Muslim World League) a Abuja.
Ministan ya ce bambance-bambancen mutanen da suka halarci taron ya nuna cewa akwai fahimtar juna, cewa tsaro, zaman lafiya da wadata a Nijeriya sun dogara ne da yadda ‘yan ƙasa za su yi aiki tare ba tare da la’akari da bambance-bambancen addini, ƙabila da siyasa ba.
Idris ya ce: “Dukkan mu muna buƙatar mu haɗa kai, mu yi tunani a matsayin ‘yan Nijeriya, mu yi tunani a matsayin ‘yan’adam, kuma mu yi aiki tare ba tare da la’akari da bambance-bambancen mu ba, domin mu kasance tsintsiya maɗaurin ki ɗaya.”
Ministan Yada Labaran ya jaddada cewa rarrabuwar kawuna bisa addini da ƙabila za su ƙara dagula yaƙi da rashin tsaro, yana mai kira ga ‘yan Nijeriya da su yi watsi da tashin hankali, rashin haƙuri da ƙoƙarin amfani da bambance-bambancen ƙasar nan wajen raba kan al’umma.
“Babu lokacin bambance-bambance. Idan a yayin yaƙin da muke yi da rashin tsaro muka bari bambance-bambancen addini suka shiga, hakan zai ƙara dagula matsalar. Buƙatar da muke da ita ta haɗa kan mu a matsayin al’umma ɗaya na da matuƙar muhimmanci,” inji shi.
Idris ya fayyace cewa ba Gwamnatin Tarayya ce ta shirya taron ba, sai dai ya ce gwamnati tana maraba da shirye-shiryen da ke inganta tattaunawa tsakanin mabiya addinai, zaman lafiya da haɗin kan ƙasa.
“Idan muna son ci gaba da tafiya zuwa ga wadata, dole ne dukkan mu mu yi tunani da aiki tare, mu kuma haɗa kai a matsayin al’umma ɗaya,” inji ministan.
Ya ce yawan al’ummar Nijeriya, muhimmancin ta da kuma tasirin ta na nufin zaman lafiya da kwanciyar hankalin ƙasar na da matuƙar tasiri ga Afirka da ma sauran sassan duniya.
“Nijeriya ƙasa ce mai matuƙar muhimmanci. Ƙasa ce mai mutane sama da miliyan 230. Zaman lafiya da kwanciyar hankali a nan na nufin zaman lafiya da kwanciyar hankali a duk faɗin Afirka, har ma da duniya baki ɗaya,” inji shi.
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, wanda ya wakilci Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a taron, ya isar da saƙon aniyar Shugaban Ƙasa ta tabbatar da ingantaccen tsaro mai ɗorewa, haɗin kan ƙasa da haɗin gwiwar ƙasa da ƙasa, yana mai cewa Nijeriya za ta ci gaba da aiki tare da abokan hulɗar ta na ƙasa da ƙasa wajen inganta zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Babban Sakataren Ƙungiyar Ƙasashen Musulmi ta Duniya kuma Shugaban Ƙungiyar Malaman Musulunci ta Duniya, Sheikh Mohammed bin Abdulkarim Al-Issa, ya buƙaci ‘yan Nijeriya da su kare haƙƙin ɗan’adam da suka yi tarayya a cikin ta, tare da yin watsi da ƙoƙarin amfani da addini, ƙabila ko talauci wajen raba kan ƙasa.
Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar III, ya yi kira da a ci gaba da tattaunawa, tsare gaskiya da ƙara ƙaimi wajen aiwatar da hanyoyin magance ƙalubalen Nijeriya, tare da kira ga ‘yan Nijeriya da su sake gina amana da ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin mabiya addinai.
A nasa jawabin, Shugaban jam’iyyar APC na Ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya buƙaci ‘yan Nijeriya da su ɗauki bambance-bambancen ƙasar a matsayin tushen ƙarfi maimakon rarrabuwar kai, yana mai cewa duk da cewa ‘yan Nijeriya suna gudanar da ibada ta hanyoyi daban-daban, suna da buri da ƙalubale iri ɗaya.
Shugaban JIBWIS na Ƙasa, Sheikh Abdullahi Bala Lau, ya yi kira da a ƙara haɗin gwiwa tsakanin gwamnati, ƙungiyoyin addini da al’ummomi wajen yaƙi da rashin tsaro, tare da ƙara zuba jari a fannin ilimi da bunƙasa ƙwarewa domin rage yiwuwar matasa su rungumi tsattsauran ra’ayi ko kuma a ɗauke su aikin laifi.
Daga cikin waɗanda suka halarci taron akwai Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, wanda ya wakilci Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu; Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani; Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi; Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum; Ministan Bunƙasa Kiwo, Idi Mukhtar Maiha; Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar III; Shugaban APC na Ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda; Sheikh Mohammed bin Abdulkarim Al-Issa; Shugaban JIBWIS na Ƙasa, Sheikh Abdullahi Bala Lau; Shugaban Majalisar Ƙoli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Nijeriya (NSCIA), da sauran manyan jami’an gwamnati, shugabannin addinai da na gargajiya, jami’an diflomasiyya, wakilan ƙungiyoyin fararen hula da sauran manyan baƙi.
Sabuwar Nigeria.







