Close Menu
    Facebook X (Twitter) Instagram
    KADA TIMESKADA TIMES
    • Home
    • News
    • Energy
    • Entertainment
    • Health
    • Politics
    • Religion
    • Sports
    • More
      • Business
      • Education
      • Environment
      • Opinion
      • Security
      • Traditional/tourism
    Subscribe
    KADA TIMESKADA TIMES
    Home » Rundunar’Yan sanda ta kubutar da mutane 75 da aka yi garkuwa da su a jihar Kaduna
    Security

    Rundunar’Yan sanda ta kubutar da mutane 75 da aka yi garkuwa da su a jihar Kaduna

    Malam Mujitaba RamalanBy Malam Mujitaba RamalanAugust 21, 20262 Mins Read
    FB IMG 1787340944545
    FB IMG 1787340944545

    Rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna ta ce ta kubutar da mutane 75 da aka yi garkuwa da su a Karamar Hukumar Birnin Gwari ta jihar.

    Kafar Sadarwar Sabuwar Nigeria ta ruwaito rundunar tana cewa wadanda aka kubutar sun hada da maza, mata da yara, wadanda wasu ’yan bindiga dauke da bindigogin AK-47 da sauran muggan makamai suka yi garkuwa da su a kauyen Folwaya da ke kusa da Birnin Gwari a ranar 19 ga Agusta, 2026.

    Jami’in hulda da jama’a na rundunar, DSP Mansir Hassan, ya ce rundunar ta samu sahihin bayanin lamarin ne daga reshen kungiyar direbobin NURTW na Birnin Gwari da misalin karfe 5:30 na yamma. Ya ce nan take aka tura wata tawagar jami’an ’yan sanda zuwa yankin.

    A cewar rundunar, ’yan bindigar sun tsere zuwa cikin daji bayan da suka hango jami’an ’yan sandan dauke da makamai, inda suka bar mutanen da suka yi garkuwa da su a wani kogo da ke cikin tsaunuka. Dukkan wadanda aka kubutar an same su cikin koshin lafiya.

    Kwamishinan ’yan sandan jihar Kaduna, CP Rabiu Muhammad, ya yaba wa reshen NURTW na Birnin Gwari bisa sanar da jami’an tsaro lamarin cikin gaggawa, tare da yabawa jami’an yankin kan daukar matakin gaggawa da kwarewa.

    Ya kuma bukaci jama’a da su ci gaba da sanya ido tare da kai rahoton duk wani abin da ake zargi ga ’yan sanda, yana mai gargadin kada jama’a su dauki doka a hannunsu. Rundunar ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da kokarin kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar.

    @75 Kaduna kidnapped police rescue victims
    Share. Facebook Twitter WhatsApp LinkedIn Email Telegram Copy Link
    Previous ArticleYadda Matakan Gyaran da Tinubu ya bullo da su,Suka Kawo Ƙarshen Matsalar Biyan Albashi A Jihohi 27
    Next Article Governor Radda Assures Ingawa Stakeholders of Continued Support

    Related Posts

    Security

    TROOPS OF OPERATION FANSAN YAMMA RESCUE KIDNAPPED VICTIM, FOIL TERRORIST ATTACK IN KADUNA, SOKOTO

    August 21, 2026
    Security

    TROOPS ARREST SUSPECTED GUNRUNNER, RESCUE KIDNAP VICTIM

    August 21, 2026
    News

    FG, Borno working to rescue 44 abducted Mussa school children

    August 21, 2026
    Add A Comment
    Leave A Reply Cancel Reply

    Latest Posts

    Governor Radda Extols Tinubu as Four Katsina Sons Clinch Federal Appointments

    April 2, 2026287 Views

    Retired Police Officers Plan “Do-or-Die” Peaceful Protest at Villa April 20

    April 5, 2026240 Views

    Emir of Katsina Approves Turbanning of Three Illustrious Sons

    April 1, 2026221 Views

    Saulawa Assumes Office as Acting Customs Provost Marshal, Promises Fair Enforcement of Discipline

    April 25, 2026164 Views

    GENERAL BABANGIDA APPLAUDS AFCSC INITIATIVE, URGES DEEPER COMMUNITY ENGAGEMENT FOR SECURITY

    May 12, 2026158 Views

    FORMER CHAIRMAN MHWUN KATSINA STATE, COMRADE MANNIR, APPEALED TO THE STATE GOVERNMENT TO FULFILLED PROMISE OF PAYING RETIRED WORKERS IN LOCAL GOVERNMENTS.

    May 12, 2026154 Views
    Stay In Touch
    • Facebook
    • YouTube
    • TikTok
    • WhatsApp
    • Twitter
    • Instagram
    © 2026 Kada Times. | Developed by ENGRMKS & CO..
    • Home
    • About Us
    • Advertise With Us
    • Privacy Policy
    • Contact Us

    Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.