Gwamnan Jihar Gombe kuma jagoran Jam’iyyar APC a jihar, Muhammadu Inuwa Yahaya, CON, ya gana da ɗan takaran Gwamna na Jam’iyyar APC, Dr. Jamilu Isiyaku Gwamna, tare da ‘yan takaran Sanata da na Majalisar Wakilai na jam’iyyar.
Wata sanarwar da babban daraktan yada labarai Na fadar gwabnatin jihar Gombe , Ismailia Uba Mislli ya bayar,ya ce hakan ya biyo bayan nasarar Dr. Jamil Gwamna ne da ƴan takaran Majalisar Dokoki na Ƙasa a matsayin ‘yan takaran Gwamna, Sanatatoci da Majalisar Wakilai da aka zaɓa a Jam’iyyar APC a zaɓen fidda gwani na kai tsaye da aka kammala kwanan nan.
Sanarwar ta ce haka kuma ganawar na zuwa ne gabanin zaɓen Fidda Gwani da Tabbatar da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a matsayin ɗan takara ɗaya tilo a zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa dake tafe, wadda aka shirya gudanarwa gobe Asabar a faɗin gundumomi 114 na jihar.
Waɗanda suka halarci taron sune DCP Mohammed Ahmed Jarman Deba (Gombe ta Tsakiya) da Mr. Jerry Joseph Damara (Gombe ta Kudu), da Hon. Usman Bello Kumo (Akko), da Hon. Ali Isa JC (Balanga/Billiri), da Hon. Sadam Bello (Gombe/Kwami/Funakaye), da Hon Inuwa Garba (Yamaltu Deba) da kuma Hon. Jamilu Ahmed Shabewa (Dukku/Nafaɗa).



