Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, murnar cika shekaru 60 a ranar 2 ga Satumba, inda ya bayyana shi a matsayin amintaccen abokin aiki da ya sadaukar da rayuwarsa wajen yi wa Borno da Najeriya hidima.
A cikin saƙon taya murnar, Shugaba Tinubu ya taya matar Shettima, Nana, da ’ya’yansa, iyalansa da abokan siyasa murnar wannan gagarumin matsayi. Ya bayyana Shettima a matsayin ɗan kishin ƙasa mai jajircewa, haƙuri da sadaukarwa, tare da yabawa irin rawar da ya taka a harkar banki da kuma lokacin da yake Gwamnan Jihar Borno.
Tinubu ya ce Shettima ya nuna jajircewa, ƙwazo da tausayi wajen inganta rayuwar al’umma a matsayinsa na Gwamnan Borno, sannan daga bisani a matsayin Mataimakin Shugaban Ƙasar Najeriya. Ya kuma yaba masa bisa biyayyarsa ga jam’iyyar APC da kuma goyon bayan da yake bai wa gwamnatin tarayya wajen aiwatar da ajandar Renewed Hope.
Shugaban ya bayyana cewa a matsayinsa na Shugaban Majalisar Tattalin Arziki ta Ƙasa (NEC), Shettima ya taka muhimmiyar rawa wajen daidaita manufofin tattalin arziki da ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohi. Ya ce mutunta kundin tsarin mulki, cibiyoyin dimokuraɗiyya, tattaunawa da tuntuba da Shettima ke yi sun taimaka wajen ƙarfafa shugabanci nagari.
Tinubu ya gode wa Mataimakin Shugaban Ƙasar bisa amincinsa da goyon bayansa, yana mai cewa zai ci gaba da aiki tare da shi wajen cika alkawuran Renewed Hope ga ’yan Najeriya. Ya kuma yi masa addu’ar Allah Ya ba shi lafiya, hikima da tsawon rai, tare da ci gaba da shiryar da shi da kuma ba shi ikon yi wa Najeriya hidima cikin nasara..

