Close Menu
    Facebook X (Twitter) Instagram
    KADA TIMESKADA TIMES
    • Home
    • News
    • Energy
    • Entertainment
    • Health
    • Politics
    • Religion
    • Sports
    • More
      • Business
      • Education
      • Environment
      • Opinion
      • Security
      • Traditional/tourism
    Subscribe
    KADA TIMESKADA TIMES
    Home » Shugaba Tinubu Ya Yi Horon ,Da A Tabbatar Da Gudanar Da Zaɓen Jihar Osun Cikin Lumana Da Adalci
    News

    Shugaba Tinubu Ya Yi Horon ,Da A Tabbatar Da Gudanar Da Zaɓen Jihar Osun Cikin Lumana Da Adalci

    Malam Mujitaba RamalanBy Malam Mujitaba RamalanAugust 15, 20262 Mins Read
    FB IMG 1786781706377
    FB IMG 1786781706377

    Daga Aliyu Samba

    Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya Bukaci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da jami’an tsaro da su tabbatar da gudanar da zaɓen gwamnan Jihar Osun cikin lumana da gaskiya.

    Al’ummar Jihar Osun za su fito rumfunan zaɓe a yau Asabar, 15 ga watan Agusta 2026, domin zaɓen wanda zai jagoranci jihar, inda ‘yan takara 15 ke neman kujerar gwamnan.

    Daga cikin ‘yan takarar akwai gwamnan jihar mai ci, Ademola Adeleke, na jam’iyyar Accord party, da ɗan takarar jam’iyyar APC, Asiwaju Munirudeen Bola Oyebamiji, da kuma ɗan takarar jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Honarabul Najeem Salaam.

    Shugaba Tinubu ya kuma buƙaci masu zaɓe a jihar da su fito su gudanar da hakkinsu na ɗan ƙasa cikin lumana, tare da guje wa duk wani abu da zai iya kawo cikas ga gudanar da zaɓen.

    Ya ce INEC na da alhakin tabbatar da cewa zaɓen ya gudana cikin tsari,da gaskiya, da ’yanci da adalci, yana mai buƙatar hukumar ta tabbatar da amincin tsarin zaɓen.

    Shugaban Ƙasar ya ce zaɓen Osun shi ne na ƙarshe cikin zaɓukan da ake gudanarwa ba tare da haɗa su da sauran zaɓuka ba kafin babban zaɓen 2027, don haka ya kamata INEC ta yi amfani da shi wajen nuna wa ’yan Najeriya shirinta na gudanar da zaɓuka masu inganci.

    Haka kuma, Shugaba Tinubu ya buƙaci Sufeto-Janar na ’Yan Sandan Najeriya da shugabannin sauran hukumomin tsaro da ke cikin aikin zaɓen da su samar da cikakken tsaro a rumfunan zaɓe domin hana masu tayar da hankali kawo cikas ga tsarin.

    Ya jaddada cewa dole ne a kare jami’an zaɓe da masu kaɗa ƙuri’a domin su gudanar da ayyukansu ba tare da tsoro ko barazana ba.

    Shugaban Ƙasar ya kuma ƙarfafa gwiwar masu zaɓe da su fito da yawa domin zaɓar ɗan takarar da suke so, yana mai cewa an ɗauki matakan da suka dace domin tabbatar da gudanar da zaɓen cikin lumana, ’yanci da adalci.

    Shugaba Tinubu ya ce sakamakon zaɓen gwamnan Osun dole ne ya kasance abin da ya bayyana ra’ayin al’ummar jihar.

    Sabuwar Nigeria

    lafiya lami osun tinubu Zaben
    Share. Facebook Twitter WhatsApp LinkedIn Email Telegram Copy Link
    Previous ArticleShugaba Tinubu Ya Rattaba Hannu Kan Dokar NPERA Ta 2026
    Next Article AFCSC JUNIOR COURSE 102/26 STUDENTS VISIT NASME, TACTICAL AIR COMMAND MAKURDI

    Related Posts

    News

    NAFC OFFICERS CHARGED TO EMBRACE INNOVATION, STAY AHEAD OF EMERGING TRENDS AS 15TH BIENNIAL TRAINING CONFERENCE CLOSES

    August 15, 2026
    News

    NPF ARRESTS, REPATRIATES CHADIAN FUGITIVE WANTED FOR MURDER IN N’DJAMENA

    August 15, 2026
    News

    Seme Customs Halts Expired Food Entry, Hands Over Seized Explosives to Police

    August 15, 2026
    Add A Comment
    Leave A Reply Cancel Reply

    Latest Posts

    Governor Radda Extols Tinubu as Four Katsina Sons Clinch Federal Appointments

    April 2, 2026283 Views

    Retired Police Officers Plan “Do-or-Die” Peaceful Protest at Villa April 20

    April 5, 2026240 Views

    Emir of Katsina Approves Turbanning of Three Illustrious Sons

    April 1, 2026220 Views

    Saulawa Assumes Office as Acting Customs Provost Marshal, Promises Fair Enforcement of Discipline

    April 25, 2026164 Views

    GENERAL BABANGIDA APPLAUDS AFCSC INITIATIVE, URGES DEEPER COMMUNITY ENGAGEMENT FOR SECURITY

    May 12, 2026157 Views

    FORMER CHAIRMAN MHWUN KATSINA STATE, COMRADE MANNIR, APPEALED TO THE STATE GOVERNMENT TO FULFILLED PROMISE OF PAYING RETIRED WORKERS IN LOCAL GOVERNMENTS.

    May 12, 2026151 Views
    Stay In Touch
    • Facebook
    • YouTube
    • TikTok
    • WhatsApp
    • Twitter
    • Instagram
    © 2026 Kada Times. | Developed by ENGRMKS & CO..
    • Home
    • About Us
    • Advertise With Us
    • Privacy Policy
    • Contact Us

    Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.