Close Menu
    Facebook X (Twitter) Instagram
    KADA TIMESKADA TIMES
    • Home
    • News
    • Energy
    • Entertainment
    • Health
    • Politics
    • Religion
    • Sports
    • More
      • Business
      • Education
      • Environment
      • Opinion
      • Security
      • Traditional/tourism
    Subscribe
    KADA TIMESKADA TIMES
    Home » Shugaban Ƙasa Bola Tinubu Ya Ƙudiri aniyyar Farfaɗo da Matatun Man Fetur Na Najeriya
    Energy

    Shugaban Ƙasa Bola Tinubu Ya Ƙudiri aniyyar Farfaɗo da Matatun Man Fetur Na Najeriya

    Malam Mujitaba RamalanBy Malam Mujitaba RamalanAugust 14, 20263 Mins Read
    FB IMG 1786700700705
    FB IMG 1786700700705

    Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ce Gwamnatin Tarayya ba za ta bari matatun man fetur na Najeriya su lalace ba, yana mai cewa za a sake fasalin yadda ake tafiyar da su ta hanyar bincike mai zurfi, sake fasalin tsarin gudanarwa da samar da ingantaccen shugabanci domin su koma aiki gadan gadan,tare da samar da riba. 

    Shugaba Tinubu ya bayyana haka ne ranar Alhamis a Abuja, lokacin da ya karɓi shugabannin Ƙungiyar Ma’aikatan Man Fetur da Iskar Gas ta Najeriya (NUPENG), ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙungiyar na ƙasa, Salimon Akanni Oladiti.

    Shugaban Ƙasar ya ce matsalolin da ke addabar matatun man fetur,za a magance su ne ta hanyar tsari mai inganci da ya dogara da hujjoji, maimakon ɗaukar matakan wucin gadi. Ya ce za a gudanar da cikakken bincike da tantancewar ƙwararru domin gano matsalolin tsarin gine-gine, aiki, kuɗi da gudanarwa da ke hana matatun samar da abin da aka gina su domin yi. Ya jaddada cewa ganin wuta da hayaƙi daga matatar mai ba shi ne ma’aunin nasara ba, sai matatar ta samar da ƙima tare da riba.

    Tinubu ya kuma ce Gwamnatin Tarayya na duba batutuwan da suka shafi aiwatar da ‘yancin cin gashin kan ƙananan hukumomi, musamman batutuwan kundin tsarin mulki da ke da alaƙa da lamarin. Ya yi kira ga masu ruwa da tsaki su fahimci matakan da ake ɗauka. Haka kuma, ya tuna da tsohon shugaban NUPENG, marigayi Frank Kokori, yana mai cewa sun yi gwagwarmayar kafa tsarin dimokuraɗiyya tare.

    Shugaban Ƙasar ya kuma yi alkawarin ƙara bai wa NUPENG damar shiga cikin aiwatar da shirin Shugaban Ƙasa na amfani da ruwan gas wato CNG, tare da ƙalubalantar ƙungiyar da ta tabbatar da cewa amfanin shirin ya isa ga masu sufuri.

    A nasa jawabin, Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, ya yaba wa NUPENG bisa amincewa da sakamakon wasu daga cikin sauye-sauyen da gwamnatin Tinubu ke aiwatarwa. Ya ce irin wannan fahimta ta taimaka wajen rage saɓani tsakanin ƙungiyoyin ƙwadago da gwamnati. Idris ya ambaci cire tallafin man fetur da kuma ayyukan gina ababen more rayuwa a faɗin ƙasar a matsayin manyan sauye-sauyen da ƙungiyar ta yaba da su.

    Shugaban NUPENG, Salimon Oladiti, ya yaba wa Tinubu kan cire tallafin man fetur, yana mai cewa matakin ya taimaka wajen dakile asarar dimbin kuɗaɗen gwamnati da kuma buɗe damar zuba jari a ababen more rayuwa. Ya kuma yaba da ayyukan manyan tituna, musamman hanyar Lagos–Calabar mai tsawon kilomita 750 da kuma babbar hanyar Sokoto–Badagry mai tsawon kilomita 1,068. Daga bisani, shugabannin NUPENG suka naɗa Tinubu a matsayin Babban Uban ƙungiyar.

    FB IMG 1786700712853
    FB IMG 1786700712853
    FB IMG 1786700706363
    FB IMG 1786700706363
    nupeng pbat visit
    Share. Facebook Twitter WhatsApp LinkedIn Email Telegram Copy Link
    Previous ArticleNIGERIA, UNITED STATES REINFORCE STRATEGIC DEFENCE AND SECURITY PARTNERSHIP AT WASHINGTON D.C. TALKS
    Next Article Radda Backs Oyebamiji at APC Mega Rally in Osogbo

    Related Posts

    Politics

    Radda Backs Oyebamiji at APC Mega Rally in Osogbo

    August 14, 2026
    Security

    COMMANDER TRAINING AND DOCTRINE COMMAND OF THE NIGERIAN ARMY COMMENDS TRAINING INNOVATIONS AT DEPOT NIGERIAN ARMY AMASIRI-EDDA

    August 13, 2026
    Security

    COMMANDER 31 ARTILLERY BRIGADE STRENGTHENS SECURITY COLLABORATION, INSPECTS TROOPS AND CRITICAL NATIONAL INFRASTRUCTURE

    August 13, 2026
    Add A Comment
    Leave A Reply Cancel Reply

    Latest Posts

    Governor Radda Extols Tinubu as Four Katsina Sons Clinch Federal Appointments

    April 2, 2026283 Views

    Retired Police Officers Plan “Do-or-Die” Peaceful Protest at Villa April 20

    April 5, 2026239 Views

    Emir of Katsina Approves Turbanning of Three Illustrious Sons

    April 1, 2026218 Views

    Saulawa Assumes Office as Acting Customs Provost Marshal, Promises Fair Enforcement of Discipline

    April 25, 2026164 Views

    GENERAL BABANGIDA APPLAUDS AFCSC INITIATIVE, URGES DEEPER COMMUNITY ENGAGEMENT FOR SECURITY

    May 12, 2026157 Views

    FORMER CHAIRMAN MHWUN KATSINA STATE, COMRADE MANNIR, APPEALED TO THE STATE GOVERNMENT TO FULFILLED PROMISE OF PAYING RETIRED WORKERS IN LOCAL GOVERNMENTS.

    May 12, 2026151 Views
    Stay In Touch
    • Facebook
    • YouTube
    • TikTok
    • WhatsApp
    • Twitter
    • Instagram
    © 2026 Kada Times. | Developed by ENGRMKS & CO..
    • Home
    • About Us
    • Advertise With Us
    • Privacy Policy
    • Contact Us

    Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.