Close Menu
    Facebook X (Twitter) Instagram
    KADA TIMESKADA TIMES
    • Home
    • News
    • Energy
    • Entertainment
    • Health
    • Politics
    • Religion
    • Sports
    • More
      • Business
      • Education
      • Environment
      • Opinion
      • Security
      • Traditional/tourism
    Subscribe
    KADA TIMESKADA TIMES
    Home » SHUGABAN KUƊI DA MULKI NA ƘARAMAR HUKUMAR FUNTUA YA GANA DA MA’AIKATA KAN TSARIN PENCOM
    News

    SHUGABAN KUƊI DA MULKI NA ƘARAMAR HUKUMAR FUNTUA YA GANA DA MA’AIKATA KAN TSARIN PENCOM

    Malam Mujitaba RamalanBy Malam Mujitaba RamalanSeptember 1, 20263 Mins Read
    IMG 20260901 WA0019
    IMG 20260901 WA0019

    Shugaban sashin Kuɗi da Mulki na Ƙaramar Hukumar Funtua, Alhaji Ibrahim Yahaya Malumfashi, ya gana da ma’aikatan ƙaramar hukumar domin bayyana musu halin da ake ciki dangane da tsarin PENCOM.

    Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwar manema labarai da Bashir YeroJami’in Watsa Labarai na Ƙaramar Hukumar Funtua ya samarwa manema labar

    Ya ce a yayin ganawar, Alhaji Ibrahim Yahaya Malumfashi ya bayyana cewa kusan dukkan ma’aikatan da ke aiki a Ƙaramar Hukumar Funtua a halin yanzu ba su shiga cikin tsarin PENCOM ba. Ya ce, bisa bayanin da aka yi musu, ma’aikatan da za su yi ritaya daga yanzu zuwa watan Nuwamba na shekarar 2055 ba su cikin wannan tsarin na Pencom.

    Saboda haka, ya yi kira ga ma’aikatan da su guji sauraron jita-jita ko yaɗa bayanan da ba su da tabbas, domin kauce wa shiga cikin ruɗani.

    Haka kuma, ya shawarci ma’aikatan da kowa ya nemi wata sana’a da zai riƙa yi domin ƙara bunƙasa tattalin arzikinsa, musamman a fannoni kamar noma, kiwo da sauran sana’o’i masu amfani.

    Shugaban sashin Kuɗi da Mulkin Alhaji Ibrahim Yahaya Malumfashi ya kuma miƙa godiyarsa ga shugaban hukumar da ke kula da horarwa da ɗaukar ma’aikatan ƙananan hukumomi ta Jihar Katsina, Alhaji Usman Mamman Maska, bisa ƙoƙarin da yake yi na horas da ma’aikata da kuma ɗora su kan tsarin aiki mai kyau domin kauce wa matsaloli yayin gudanar da ayyukansu na gwamnati.

    Haka kuma, ya gode wa Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda, bisa yadda gwamnatin jihar ke biyan albashi, fansho da sauran haƙƙoƙin ma’aikatan ƙananan hukumomi a kan lokaci.

    A nasa jawabin, Daraktan Sashen Kula da Ma’aikata (Personnel Management Department), Alhaji Lawal Aliyu Faskari, ya bayyana cewa an kira su zuwa Katsina, inda aka yi musu cikakken bayani kan yadda tsarin PENCOM yake.

    Ya ce, wannan ne ya sa aka kira taron ma’aikatan domin a bayyana musu tsarin a hukumance, tare da fayyace duk wasu bayanai da suka shafi tsarin, domin kauce wa yaɗuwar jita-jita da ruɗani.

    Alhaji Lawal Aliyu Faskari ya kuma gargadi ma’aikatan da su guji yin rubuce-rubuce ko wallafa bayanai a kafafen sada zumunta ba tare da dalili ko cikakken bayani ba, domin yin hakan na iya jawo wa mutum matsala.

    IMG 20260901 WA0024
    IMG 20260901 WA0024
    IMG 20260901 WA0023
    IMG 20260901 WA0023
    IMG 20260901 WA0022
    IMG 20260901 WA0022
    IMG 20260901 WA0021
    IMG 20260901 WA0021
    IMG 20260901 WA0020
    IMG 20260901 WA0020
    IMG 20260901 WA0019
    IMG 20260901 WA0019
    IMG 20260901 WA0017
    IMG 20260901 WA0017
    IMG 20260901 WA0018
    IMG 20260901 WA0018
    administration brief director finance Funtua workers
    Share. Facebook Twitter WhatsApp LinkedIn Email Telegram Copy Link
    Previous ArticleGovernor Abba Kabir Yusuf Urges Parents, Clerics, and Stakeholders to Unite Against Youth Restiveness, Immorality, and Substance Abuse
    Next Article LG polls : YSIEC begins screening of candidates

    Related Posts

    Business

    Gov. Buni Lauds Yobe Microfinance Bank…You Have Justified Govt. Investments

    September 1, 2026
    News

    Maulud,Radda attends maulud at Katsina Chief Imam residence.

    September 1, 2026
    News

    NDC Governorship Candidate Condemns Bandit Attacks in Four Kano LGAs, Demands Urgent Security Action

    September 1, 2026
    Add A Comment
    Leave A Reply Cancel Reply

    Latest Posts

    Governor Radda Extols Tinubu as Four Katsina Sons Clinch Federal Appointments

    April 2, 2026294 Views

    Retired Police Officers Plan “Do-or-Die” Peaceful Protest at Villa April 20

    April 5, 2026242 Views

    Emir of Katsina Approves Turbanning of Three Illustrious Sons

    April 1, 2026225 Views

    Saulawa Assumes Office as Acting Customs Provost Marshal, Promises Fair Enforcement of Discipline

    April 25, 2026168 Views

    GENERAL BABANGIDA APPLAUDS AFCSC INITIATIVE, URGES DEEPER COMMUNITY ENGAGEMENT FOR SECURITY

    May 12, 2026164 Views

    FORMER CHAIRMAN MHWUN KATSINA STATE, COMRADE MANNIR, APPEALED TO THE STATE GOVERNMENT TO FULFILLED PROMISE OF PAYING RETIRED WORKERS IN LOCAL GOVERNMENTS.

    May 12, 2026156 Views
    Stay In Touch
    • Facebook
    • YouTube
    • TikTok
    • WhatsApp
    • Twitter
    • Instagram
    © 2026 Kada Times. | Developed by ENGRMKS & CO..
    • Home
    • About Us
    • Advertise With Us
    • Privacy Policy
    • Contact Us

    Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.