Daga Aliyu Samba
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin karkatar da kuɗaɗen da Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta kwato zuwa Asusun Bayar da Lamunin Karatu na Nijeriya (NELFUND), domin ƙara ƙarfafa shirin bayar da lamunin karatu ga ɗaliban ƙasar.
Kafar Sadarwar Sabuwar Nigeria ta ce Ministan Ilimi, Dr Tunji Alausa, ne ya bayyana hakan a ranar Laraba yayin da yake yi wa manema labarai bayani a Fadar Shugaban Ƙasa bayan kammala taron Majalisar Zartarwa ta Ƙasa (FEC).
Ya ce Majalisar ta kuma amince da karkatar da wasu kuɗaɗen da ba a karɓa ba, ciki har da kuɗaɗen riba (dividends) da ba a karɓa ba da ke cikin kasuwanin hada hadar jari,Capital Market Trust Fund da kuma irin asusun ajiyar kudaden nan da masu su suka daina aiki da su,Dormant Account Trust Fund, zuwa shirin lamunin karatu.
Alausa ya ce matakin na daga cikin ƙoƙarin Gwamnatin Tarayya na tabbatar da samun isassun kuɗaɗe da za su ba NELFUND damar faɗaɗa shirin da kuma tabbatar da cewa ɗaliban da ke buƙatar tallafin kuɗin karatu sun samu damar ci gaba da karatunsu.
Ministan ya ƙara da cewa amfani da waɗannan kuɗaɗe zai taimaka wajen ƙara ɗorewar tsarin bayar da lamunin karatu, tare da rage matsalolin kuɗi da ke iya hana wasu ɗalibai ci gaba da karatu a manyan makarantu.
Gwamnatin Tarayya ta kafa NELFUND ne domin samar da tallafin kuɗi ga ɗaliban manyan makarantu, musamman waɗanda ke fuskantar matsalar biyan kuɗaɗen karatu.
Sabon matakin na zuwa ne yayin da gwamnati ke ci gaba da faɗaɗa shirin lamunin karatu domin ƙara yawan ɗaliban da za su iya cin gajiyarsa a faɗin Nijeriya.

