Mataimakin Shugaban Najeriya, Sanata Kashim Shettima, ya ce burin gwamnatin tarayya na gina tattalin arzikin Najeriya mai darajar dala tiriliyan daya ba zai tabbata ba matukar ba a bai wa mata cikakkiyar dama su taka rawa a harkokin tattalin arzikin kasar ba.
Kafar Sadarwar Sabuwar Nigeria ta ce Shettima ya bayyana haka ne ranar Laraba a Abuja, yayin taron kasa na biyu kan hada mata da harkokin tattalin arziki, #SheIsIncluded 2026, inda ya ce gwamnati ta kaddamar da wasu tsare-tsare guda hudu domin rage gibin da ke tsakanin maza da mata wajen samun damar harkokin kudi. Ya ce kashi 47 cikin 100 na matan Najeriya ne ke da asusun kudi na zamani, idan aka kwatanta da kashi 58 cikin 100 na maza.
Ya ce gwamnati ta mayar da hankali wajen hada mata da matasa da ilimi, jari, kasuwanni da sabbin damammakin tattalin arziki, tare da jaddada cewa zuba jari a mata ba taimako na jin kai ba ne, dabarar bunkasa tattalin arziki ce. A nata bangaren, Ministar Harkokin Mata da Ci gaban Al’umma, Hajiya Imaan Sulaiman-Ibrahim, ta ce burin dala tiriliyan daya ba zai cika ba idan ba a shigar da mata, musamman wadanda ke aiki a bangaren tattalin arzikin karkara da na yau da kullum, cikin shirin sauyin tattalin arzikin kasar ba.
Ministar ta kuma bayyana cewa shirin Nigeria for Women Programme Scale-Up ya fadada tsarin kungiyoyin mata zuwa mata miliyan 4.5 da aka tsara cikin kungiyoyi 300,000 a fadin Najeriya. Ta ce a matakin farko, an hada mata sama da 560,000 cikin kungiyoyi fiye da 26,000, inda suka tara sama da Naira biliyan 4.9 daga albarkatun kansu tare da samun tallafin rayuwa na kusan Naira biliyan 15.6. Haka kuma, gwamnati ta bayyana wasu tsare-tsare hudu da suka hada da samar da tsarin amintaccen amfani da fasahar zamani, amfani da bayanai wajen tabbatar da gaskiya, hadin gwiwar samar da kudade da National Income Activation Initiative domin mayar da hada mata da harkokin kudi zuwa samar da kudin shiga da ayyukan yi..





