Close Menu
    Facebook X (Twitter) Instagram
    KADA TIMESKADA TIMES
    • Home
    • News
    • Energy
    • Entertainment
    • Health
    • Politics
    • Religion
    • Sports
    • More
      • Business
      • Education
      • Environment
      • Opinion
      • Security
      • Traditional/tourism
    Subscribe
    KADA TIMESKADA TIMES
    Home » Tattalin arzikin Najeriya na ƙara Habbaka da bunƙasa inda ya nufi dala tiriliyan ɗaya
    Business

    Tattalin arzikin Najeriya na ƙara Habbaka da bunƙasa inda ya nufi dala tiriliyan ɗaya

    Malam Mujitaba RamalanBy Malam Mujitaba RamalanSeptember 1, 20262 Mins Read
    FB IMG 1788290575320
    FB IMG 1788290575320

    Tattalin arzikin Najeriya ya ci gaba da samun bunƙasa a zango na biyu na shekarar 2026, inda GDP ɗin ƙasar ya ƙaru da kashi 4.43 cikin 100, idan aka kwatanta da kashi 4.23 a makamancin wannan lokaci na shekarar 2025 da kuma kashi 3.89 a zangon farko na 2026, a cewar Ma’aikatar Kuɗin Tarayya.

    Ma’aikatar ta ce wannan ci gaban ya ɗaga matsakaicin bunƙasar tattalin arzikin ƙasar a farkon rabin shekarar 2026 zuwa kashi 4.16 cikin 100, daga kashi 3.68 da aka samu a makamancin wannan lokacin shekarar 2025. Ta ce kuma ci gaban ya fara yaɗuwa zuwa sassa daban-daban, inda sassa 27 na tattalin arzikin ƙasar suka samu bunƙasar sama da kashi uku a zangon na biyu, idan aka kwatanta da 23 a bara.

    A fannin samar da kayayyaki, masana’antu sun samu bunƙasa da kashi 3.24 cikin 100, daga kashi 1.60 a zangon makamancin wannan na shekarar 2025, yayin da noma ya ƙaru da kashi 4.39 daga kashi 2.82. Haka kuma, ɓangaren ayyuka, wanda shi ne mafi girma wajen tallafa wa tattalin arzikin ƙasar, ya bunƙasa da kashi 4.60 daga kashi 3.94.

    Ma’aikatar ta kuma ce ƙarin darajar naira da daidaito a kasuwar canjin kuɗi sun taimaka wajen ƙara darajar tattalin arzikin Najeriya idan aka auna shi da dalar Amurka. A cewarta, naira ta samu ƙarin daraja da sama da kashi 12 cikin 100 tsakanin farkon rabin shekarar 2025 da na 2026, lamarin da ya taimaka wajen ƙara darajar tattalin arzikin ƙasar da kusan kashi 17 cikin 100 a ma’aunin dalar Amurka.

    Ma’aikatar Kuɗin ta ce wannan ci gaba na nuna cewa Najeriya na kan hanyar cimma burin Gwamnatin Tarayya na mayar da tattalin arzikin ƙasar ya kai dala tiriliyan ɗaya nan da shekarar 2030. Ta ce Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF) ya sanya Najeriya cikin ƙasashe 10 da ake sa ran za su fi bayar da gudunmawa ga bunƙasar tattalin arzikin duniya a 2026, yayin da gwamnati ta jaddada buƙatar ci gaba da sauye-sauyen tattalin arziki domin tabbatar da cewa ci gaban ya koma ga talakawa da sauran ‘yanƙasa.

    Sabuwar Nigeria

    economy fast gdpe growing nigerian
    Share. Facebook Twitter WhatsApp LinkedIn Email Telegram Copy Link
    Previous ArticleEXERCISE SHINING STAR 2026: NAWC ORGANISES INTER-AGENCY LECTURES FOR FEMALE PERSONNEL
    Next Article VC Bunkure Receives Former Coursemates from ABU

    Related Posts

    Business

    Gov. Buni Lauds Yobe Microfinance Bank…You Have Justified Govt. Investments

    September 1, 2026
    Business

    GOVERNOR LAWAL SPEAKS AT 2026 CEO FORUM ON UNLOCKING INVESTMENTS IN ZAMFARA

    September 1, 2026
    Business

    Yadda Najeriya Ta bunkasa kudaden Ajiyar kasashen Waje Daga Dala Biliyan 35 Zuwa 52.5

    August 22, 2026
    Add A Comment
    Leave A Reply Cancel Reply

    Latest Posts

    Governor Radda Extols Tinubu as Four Katsina Sons Clinch Federal Appointments

    April 2, 2026294 Views

    Retired Police Officers Plan “Do-or-Die” Peaceful Protest at Villa April 20

    April 5, 2026242 Views

    Emir of Katsina Approves Turbanning of Three Illustrious Sons

    April 1, 2026225 Views

    Saulawa Assumes Office as Acting Customs Provost Marshal, Promises Fair Enforcement of Discipline

    April 25, 2026168 Views

    GENERAL BABANGIDA APPLAUDS AFCSC INITIATIVE, URGES DEEPER COMMUNITY ENGAGEMENT FOR SECURITY

    May 12, 2026164 Views

    FORMER CHAIRMAN MHWUN KATSINA STATE, COMRADE MANNIR, APPEALED TO THE STATE GOVERNMENT TO FULFILLED PROMISE OF PAYING RETIRED WORKERS IN LOCAL GOVERNMENTS.

    May 12, 2026156 Views
    Stay In Touch
    • Facebook
    • YouTube
    • TikTok
    • WhatsApp
    • Twitter
    • Instagram
    © 2026 Kada Times. | Developed by ENGRMKS & CO..
    • Home
    • About Us
    • Advertise With Us
    • Privacy Policy
    • Contact Us

    Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.