Close Menu
    Facebook X (Twitter) Instagram
    KADA TIMESKADA TIMES
    • Home
    • News
    • Energy
    • Entertainment
    • Health
    • Politics
    • Religion
    • Sports
    • More
      • Business
      • Education
      • Environment
      • Opinion
      • Security
      • Traditional/tourism
    Subscribe
    KADA TIMESKADA TIMES
    Home » Tinubu Ya Amince da Ƙarin Albashi Har Kashi 80 Ga Jami’an Sojin Najeriya
    News

    Tinubu Ya Amince da Ƙarin Albashi Har Kashi 80 Ga Jami’an Sojin Najeriya

    Malam Mujitaba RamalanBy Malam Mujitaba RamalanAugust 5, 20262 Mins Read
    FB IMG 1785918480716
    FB IMG 1785918480716

    Daga Aliyu Samba

    Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da ƙarin albashi ga jami’an Rundunar Sojin Najeriya da ya kai tsakanin kashi 30 zuwa 80 cikin ɗari, a wani mataki da gwamnatin tarayya ta ce na inganta jin daɗin jami’an tsaro da ƙarfafa musu gwiwa wajen gudanar da ayyukansu.

    Sanarwar da Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Yaɗa Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Talata ta bayyana cewa kimanin jami’ai da sojoji 250,000 ne za su amfana da sabon tsarin albashin, wanda zai fara aiki daga 1 ga Satumban 2026.

    A cewar sanarwar, jami’an da ke daga mukamin Brigadier Janar zuwa Janar za su samu ƙarin albashi na kashi 30 cikin ɗari, yayin da jami’an daga mukamin Kanal zuwa Warrant Officer za su samu ƙarin kashi 50 cikin ɗari. Haka kuma, sojojin da ke daga mukamin Private zuwa Staff Sergeant za su amfana da ƙarin albashi mafi girma na kashi 80 cikin ɗari.

    Sanarwar ta ƙara da cewa sabon tsarin zai ƙara yawan kuɗin da gwamnati ke kashewa kan albashin jami’an sojin daga Naira biliyan 660 zuwa Naira biliyan 924 a duk shekara.

    Shugaba Tinubu ya ce gwamnatinsa na yaba wa jajircewa da sadaukarwar jami’an rundunar sojin wajen yaƙi da matsalolin tsaro da suka haɗa da ta’addanci, garkuwa da mutane da kuma ayyukan ‘yan bindiga a wasu sassan ƙasar.

    Ya ce, “Mazan da matan da ke tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyinmu sun cancanci a tallafa musu tare da nuna musu godiya saboda hidimar da suke yi wa ƙasa. Gwamnatinmu za ta ci gaba da ba da fifiko ga jin daɗin jami’an tsaro tare da samar musu da makamai da fasahohin zamani domin su gudanar da aikinsu yadda ya kamata.”

    Shugaban ya kuma jaddada cewa babu wata ƙasa da za ta iya samun ci gaba mai ɗorewa ba tare da ingantaccen tsaro ba, yana mai tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen amfani da dukkan rundunonin tsaro domin kawar da barazanar tsaro da kare rayuka da dukiyoyin ‘yan Najeriya.

    Tinubu ya kuma yi kira ga jami’an rundunar sojin da su ɗauki wannan ƙarin albashi a matsayin wata alamar godiya daga gwamnati bisa irin hidimar da suke yi wa ƙasa, yana mai bayyana ƙwarin gwiwar cewa Najeriya za ta yi nasara kan masu neman tada zaune tsaye da tarwatsa zaman lafiyar ƙasar

    Sabuwar Nigeria.

    albashi karin sojoji
    Share. Facebook Twitter WhatsApp LinkedIn Email Telegram Copy Link
    Previous ArticleFARMER GOVERNOR BAGO HOLDS DISCUSSIONS WITH PRIVATE FIRM ON PROPOSED CNG INFRASTRUCTURE INVESTMENT.
    Next Article CORPS COMMANDER ORDNANCE VISITS ARMY CENTRAL AMMUNITION DEPOT AGUNU

    Related Posts

    News

    Governor Radda Approves Release of ₦4 Billion for Second Phase of Community Development Programme

    August 5, 2026
    News

    *Kano League of Veteran Journalists Rallies Behind Gov Yusuf’s Drug Abuse Task Force, Pledges Full Support*

    August 5, 2026
    News

    Governor Radda Swears in Four Permanent Secretaries

    August 5, 2026
    Add A Comment
    Leave A Reply Cancel Reply

    Latest Posts

    Governor Radda Extols Tinubu as Four Katsina Sons Clinch Federal Appointments

    April 2, 2026279 Views

    Retired Police Officers Plan “Do-or-Die” Peaceful Protest at Villa April 20

    April 5, 2026236 Views

    Emir of Katsina Approves Turbanning of Three Illustrious Sons

    April 1, 2026215 Views

    Saulawa Assumes Office as Acting Customs Provost Marshal, Promises Fair Enforcement of Discipline

    April 25, 2026161 Views

    GENERAL BABANGIDA APPLAUDS AFCSC INITIATIVE, URGES DEEPER COMMUNITY ENGAGEMENT FOR SECURITY

    May 12, 2026157 Views

    FORMER CHAIRMAN MHWUN KATSINA STATE, COMRADE MANNIR, APPEALED TO THE STATE GOVERNMENT TO FULFILLED PROMISE OF PAYING RETIRED WORKERS IN LOCAL GOVERNMENTS.

    May 12, 2026151 Views
    Stay In Touch
    • Facebook
    • YouTube
    • TikTok
    • WhatsApp
    • Twitter
    • Instagram
    © 2026 Kada Times. | Developed by ENGRMKS & CO..
    • Home
    • About Us
    • Advertise With Us
    • Privacy Policy
    • Contact Us

    Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.