Close Menu
    Facebook X (Twitter) Instagram
    KADA TIMESKADA TIMES
    • Home
    • News
    • Energy
    • Entertainment
    • Health
    • Politics
    • Religion
    • Sports
    • More
      • Business
      • Education
      • Environment
      • Opinion
      • Security
      • Traditional/tourism
    Subscribe
    KADA TIMESKADA TIMES
    Home » Tinubu ya ba da umurnin a tsara sabbin dabarun tabbatar da shirin tsaron Najeriya na
    Security

    Tinubu ya ba da umurnin a tsara sabbin dabarun tabbatar da shirin tsaron Najeriya na

    Malam Mujitaba RamalanBy Malam Mujitaba RamalanAugust 19, 20262 Mins Read
    FB IMG 1787169266127
    FB IMG 1787169266127

    Daga Aliyu Samba

    Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya umarci mai ba shi shawara na musamman kan tsaron cikin gida, Manjo Janar Adeyinka A. Famadewa, da ya jagoranci aikin samar da cikakken rahoton barazanar tsaro da kuma shirin ayyukan tsaro na shekaru biyar.

    Kafar Sadarwar Sabuwar Nigeria ta ce Shugaban ya bayar da umarnin ne domin kara inganta hadin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro, da na leken asiri da kuma rundunonin sojin kasar.

    Tinubu ya kafa kwamiti mai mambobi 11 domin shirya shirin, wanda ya hada da mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu; Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa; da Karamin Ministan Tsaro, Bello Muhammad Matawalle. Sauran mambobin sun hada da Shugaban Hafsan Tsaro, Janar Olufemi Oluyede; Shugaban Sojin Kasa, Laftanar Janar Waidi Shaibu; Shugaban Sojin Sama, Air Marshal Sunday Kelvin Aneke; da Shugaban Sojin Ruwa, Vice Admiral Idi Abbas.

    Daraktocin DSS, Tosin Ajayi, da Hukumar Leken Asiri ta Kasa, Ambasada Muhammed Muhammed, na cikin kwamitin.

    Shugaban ya bayar da umarnin ne a taron Majalisar Zartarwa ta Tarayya da aka gudanar ranar Laraba a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja, inda ya ce ana bukatar tsari guda daya da zai bai wa hukumomin tsaro damar tunkarar sauye-sauyen barazanar tsaro da ke fuskantar kasar.

    Shugaban ya ce rahoton Tantance Manyan Barazanar Tsaron Ƙasa (National Threat Assessment) zai gano manyan barazanar da ke fuskantar Najeriya, tare da tantance su da kuma tsara manufofin tunkarar su

    Ya ce shirin Tsarin Dabarun Ayyukan Tsaron Ƙasa (Strategic Defence Operations Plan) kuma zai fayyace abubuwan da ya kamata a bai wa fifiko, irin rundunonin da ake bukata a wurare daban-daban, gibin kayan aiki da sauran bukatun soji, da kuma lokacin aiwatar da shirin.

    Tinubu ya umarci kwamitin da ya fara aiki nan take tare da kammala rahoton barazanar tsaro da shirin ayyukan tsaro na shekaru biyar cikin kwanaki 90 domin gabatar da su gare shi. Ya ce bayan amincewa, shirin zai zama babban tsarin da za a yi amfani da shi wajen tsara ayyukan soji da tsaro na wani lokaci, da kuma kafa tsarin kashe kudaden tsaro da sayen kayan aikin soja na shekaru masu zuwa.

    charges new on pbat roadmap security
    Share. Facebook Twitter WhatsApp LinkedIn Email Telegram Copy Link
    Previous ArticleBa za a cimma burin samun tattalin arzikin dala tiriliyan daya ba ,sai an sa mata cikin tsare tsaren — Shettima
    Next Article Chairman Lake Chad Basin Governors’ Forum Gov. Mai Mala Buni Visits Nigerian Refugees in Kaya, Chad.

    Related Posts

    Security

    TINUBU TASKS HOMELAND SECURITY ADVISER TO COORDINATE FIVE-YEAR NATIONAL SECURITY THREAT ASSESSMENT, DEFENCE PLAN

    August 19, 2026
    Security

    IGP DISU ATTENDS NORTH-WEST SECURITY SUMMIT, CALLS FOR COORDINATED REGIONAL RESPONSE TO INSECURITY

    August 19, 2026
    Security

    Police, DSS chiefs laud ABU security apparatus

    August 19, 2026
    Add A Comment
    Leave A Reply Cancel Reply

    Latest Posts

    Governor Radda Extols Tinubu as Four Katsina Sons Clinch Federal Appointments

    April 2, 2026285 Views

    Retired Police Officers Plan “Do-or-Die” Peaceful Protest at Villa April 20

    April 5, 2026240 Views

    Emir of Katsina Approves Turbanning of Three Illustrious Sons

    April 1, 2026220 Views

    Saulawa Assumes Office as Acting Customs Provost Marshal, Promises Fair Enforcement of Discipline

    April 25, 2026164 Views

    GENERAL BABANGIDA APPLAUDS AFCSC INITIATIVE, URGES DEEPER COMMUNITY ENGAGEMENT FOR SECURITY

    May 12, 2026158 Views

    FORMER CHAIRMAN MHWUN KATSINA STATE, COMRADE MANNIR, APPEALED TO THE STATE GOVERNMENT TO FULFILLED PROMISE OF PAYING RETIRED WORKERS IN LOCAL GOVERNMENTS.

    May 12, 2026154 Views
    Stay In Touch
    • Facebook
    • YouTube
    • TikTok
    • WhatsApp
    • Twitter
    • Instagram
    © 2026 Kada Times. | Developed by ENGRMKS & CO..
    • Home
    • About Us
    • Advertise With Us
    • Privacy Policy
    • Contact Us

    Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.