Close Menu
    Facebook X (Twitter) Instagram
    KADA TIMESKADA TIMES
    • Home
    • News
    • Energy
    • Entertainment
    • Health
    • Politics
    • Religion
    • Sports
    • More
      • Business
      • Education
      • Environment
      • Opinion
      • Security
      • Traditional/tourism
    Subscribe
    KADA TIMESKADA TIMES
    Home » WAKILIN BUNGUDU/MARU A MAJALISAR TARAYYA ZANNAN BUNGUDU YA ZIYARCI SANSANONAN JAMI’AN SOJI DAKE DANSADAU, MAGAMI DA DARAGA/DANKURMI
    Security

    WAKILIN BUNGUDU/MARU A MAJALISAR TARAYYA ZANNAN BUNGUDU YA ZIYARCI SANSANONAN JAMI’AN SOJI DAKE DANSADAU, MAGAMI DA DARAGA/DANKURMI

    Malam Mujitaba RamalanBy Malam Mujitaba RamalanJune 10, 20263 Mins Read
    FB IMG 1781099297384
    FB IMG 1781099297384

    A wani bangare na bada kulawa ga sha’anin tsaro a cikin wakilcin sa Danmajalisar Tarayyar mai kula da Kananan Hukumomin Bungudu/Maru Hon. Dakta Abdulmalik Zubairu Zannan Bungudu ya ziyarci sansanonan JAMI’AN SOJI dake yankunan Dansadau da Magami da kuma Daraga/Dankurmi dukkan su a cikin yankin da yake yiwa wakilci.

    Wannan bayanin yana kunshe ne cikin wata sanarwar manema labarai da Mai Magana da yawun Dan majalisar,Jakadan bungudu, Aminu Lawal bungudu ya rabawa manema labarai.

    Sanarwar ta ce, Ziyarar sansanonan wadda ta gudana a kwanan nan ta biyo bayan kokarin Wakilin na karfafawa sha’anin tsaron al’ummar sa musamman a wadannan yankuna da ayukkan yan bindiga ke yiwa barazana babu dare babu rana.

    A cikin jawabin sa a dukkan wuraren da ya ziyarta, Zannan Bungudu ya karfafa wa zaratan JAMI’AN SOJIN guiwa akan yadda suke kokarin kare rayukka da dukiyyoyin al’umma, yana mai cewa matsalar tsaro na daga cikin abinda wakilcin sa yake baiwa fifikon gaske.

    Zannan Bungudu ya bukaci Jami’an Sojin da kada suyi kasa a guiwa wajen gudanar da aikin su tare da shaida masu cewar a shirye yake ya tallafa ga dukkan bukatocin su gwaegwadon hali a duk lokacin da aka gabatar masa.

    Ya jajanta masu akan yadda ayukkan yan bindiga ke ta’adi ga Jami’an su, yana mai tabbatar masu cewa duk wanda ya rasa rayuwa a cikin wannan aiki babu shakka yana da kyakkyawan sakamo a gobe Kiyama.

    Sai dai ya bukaci al’umma da su bada cikakken hadin kai ga Jami’an tsaron domin kakkabe ayukkan yan ta’addan.

    Yawaitar ayukkan yan bindiga da yanayin yadda tattalin arzikin wadannan yankuna yaci karo da koma baya shine ya haifar da Wakilin ya bada umarnin cigaba da daukar nauyin dukkan al’ummar da yan bindigar suka yiwa rauni ba tare da jinkiri ko la’akari da inda suka fito ba.

    Ziyartar wadannan yankuna dake fama da matsalar tsaro da Zannan Bungudu ke yi ya zame masa dabi’a tun bayan zaman sa Wakilin al’umma a shekarar 2015.

    Idan za’a iya tunawa, bukata ta farko da Zannan Bungudu ya gabatarwa Majalisar tarayya a shekarar 2015 ita ce bukatar inganta tsaro a wadannan yankuna lamarin da haifar da aka aiwatar da shirin atisayen Jami’an Sojin Nijeriya na shekarar a yankin Dansadau.

    Tuni dai da Wakilin ya dawo gida bayan kwashe kwanaki biyu na wannan ziyara a wadannan yankuna.

    Allah SWT Ya dawo muna da zaman lafiyar mu hadi da Yalwar arziki.

     

    FB IMG 1781099290096
    FB IMG 1781099290096
    FB IMG 1781099272507
    FB IMG 1781099272507
    FB IMG 1781099262595
    FB IMG 1781099262595

     

     

     

    bungudu dansadau maru member visit
    Share. Facebook Twitter WhatsApp LinkedIn Email Telegram Copy Link
    Previous ArticleVillage Head of Panhauya calls on ABU Vice-Chancellor
    Next Article Students Excited as VC Inspects Conduct of Examinations at CBT Centres

    Related Posts

    Security

    NIGERIA POLICE FORCE REPATRIATES WANTED WILDLIFE TRAFFICKER TO SHANGHAI, PEOPLE’S REPUBLIC OF CHINA

    July 30, 2026
    Security

    NATIONAL DEFENCE COLLEGE PRESENTS STRATEGIC BLUEPRINT TO COAS FOR STRENGTHENING NIGERIAN ARMY’S NCO CORPS

    July 29, 2026
    Security

    NIGERIAN ARMY HONOURED AS AFRICA’S PREMIER COUNTER-TERRORISM FORCE

    July 29, 2026
    Add A Comment
    Leave A Reply Cancel Reply

    Latest Posts

    Governor Radda Extols Tinubu as Four Katsina Sons Clinch Federal Appointments

    April 2, 2026275 Views

    Retired Police Officers Plan “Do-or-Die” Peaceful Protest at Villa April 20

    April 5, 2026235 Views

    Emir of Katsina Approves Turbanning of Three Illustrious Sons

    April 1, 2026211 Views

    Saulawa Assumes Office as Acting Customs Provost Marshal, Promises Fair Enforcement of Discipline

    April 25, 2026159 Views

    GENERAL BABANGIDA APPLAUDS AFCSC INITIATIVE, URGES DEEPER COMMUNITY ENGAGEMENT FOR SECURITY

    May 12, 2026155 Views

    FORMER CHAIRMAN MHWUN KATSINA STATE, COMRADE MANNIR, APPEALED TO THE STATE GOVERNMENT TO FULFILLED PROMISE OF PAYING RETIRED WORKERS IN LOCAL GOVERNMENTS.

    May 12, 2026150 Views
    Stay In Touch
    • Facebook
    • YouTube
    • TikTok
    • WhatsApp
    • Twitter
    • Instagram
    © 2026 Kada Times. | Developed by ENGRMKS & CO..
    • Home
    • About Us
    • Advertise With Us
    • Privacy Policy
    • Contact Us

    Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.