Ministan Kasafin Kuɗi da Tsare-tsaren Tattalin Arziƙi, Sanata Abubakar Atiku Bagudu, ya kai ziyarar gani da ido a yau Litinin, 17 ga Agusta, 2026, domin duba yadda aikin Babbar Hanyar Sokoto–Badagry ke gudana a yankin jihar Kebbi.
Sabuwar Nigeria ta ruwaito Ministan yana yabawa da ƙoƙarin ma’aikatan, tare da ƙarfafa gwiwarsu wajen ci gaba da aikin.
Read also: Zuru Emirate Development Society Dissolves Executives,
Hanyar na daga cikin muhimman ayyukan Renewed Hope Agenda na Shugaba Bola Ahmed Tinubu, kuma ana sa ran kammala hanyar zai sauƙaƙa zirga-zirga tsakanin Arewa da Kudu maso Yamma, da kuma rage lokacin tafiya, da bunƙasa kasuwanci.






