Close Menu
    Facebook X (Twitter) Instagram
    KADA TIMESKADA TIMES
    • Home
    • News
    • Energy
    • Entertainment
    • Health
    • Politics
    • Religion
    • Sports
    • More
      • Business
      • Education
      • Environment
      • Opinion
      • Security
      • Traditional/tourism
    Subscribe
    KADA TIMESKADA TIMES
    Home » Tinubu zai yi wa shugabannin duniya jawabi a babban Taron Majalisar Dinkin Duniya ranar 23 ga Satumba
    News

    Tinubu zai yi wa shugabannin duniya jawabi a babban Taron Majalisar Dinkin Duniya ranar 23 ga Satumba

    Malam Mujitaba RamalanBy Malam Mujitaba RamalanAugust 19, 20262 Mins Read
    FB IMG 1787169388997
    FB IMG 1787169388997

    Shugaba Bola Ahmed Tinubu, zai shiga cikin Jerin shugabannin kasashen duniya wajen gabatar da jawabi a babban taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 81 (UNGA 81) a birnin New York, Amurka, ranar Laraba, 23 ga Satumba, 2026.

    Kafar Sadarwar Sabuwar Nigeria,ta ce an tsara Tinubu zai kasance mai magana na 10 a zaman safiyar rana ta biyu, inda ake sa ran zai yi jawabinsa tsakanin karfe 11:30 na safe zuwa 12:00 na rana agogon New York, wato tsakanin karfe 4:30 zuwa 5:00 na yamma agogon Najeriya. Sama da shugabannin kasashe 193 ne ake sa ran Za su halarci wannan babban Taron.

    Taron Na bana, wanda za a gudanar daga 22 zuwa 28 ga Satumba, zai mayar da hankali kan taken “Restoring trust, managing transformation: A United Nations that delivers for all”, wato dawo da Aminci,da kula da sauye sauye,a tsarin majalisar dinkin duniya ta kowa da kowa.

    Ana kuma sa ran Tinubu zai halarci tarurruka da dama da suka shafi sauyin yanayi, hauhawar ruwan teku da shirin tunkarar annobar cututtuka, tare da ganawa da babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya mai barin gado, António Guterres.

    Babban Jakadan Najeriya a Majalisar Dinkin Duniya, Jimoh Ibrahim, ya tabbatar da halartar Tinubu, yana mai cewa shugaban zai yi amfani da taron wajen bayyana sauye-sauyen da gwamnatinsa ke aiwatarwa tare da neman hadin kan kasashen duniya kan tsaron iyakokin Afirka ta Yamma. Ya kuma bayyana yiwuwar ganawar Tinubu da shugaban Amurka, Donald Trump, a gefen taron. Ana sa ran zaman muhawarar babban taron zai gudana daga 22 zuwa 28 ga Satumba, yayin da taron Majalisar Dinkin Duniya na 81 zai bude a hukumance tun daga 8 ga Satumba.

    amurka babban mdd pbat taron
    Share. Facebook Twitter WhatsApp LinkedIn Email Telegram Copy Link
    Previous ArticleZAMFARA HOSTS POLICE SECURITY SUMMIT AS GOVERNOR LAWAL VOWS NO NEGOTIATION WITH BANDITS
    Next Article Taimakawa Dalibai: Shugaba Tinubu ya ba da umurnin a mayar da kuɗaɗen da EFCC ta kwato zuwa hukumar ba da tallafin karatun Dalibai,NELFUND

    Related Posts

    News

    PRESIDENT TINUBU APPOINTS ABEL OLUMUYIWA ENITAN AS HEAD OF THE CIVIL SERVICE OF THE FEDERATION

    August 20, 2026
    News

    Governor Radda Applauds KNYDAI’s Confidence in Tinubu’s Renewed Hope, 1,500-Beneficiary Empowerment

    August 20, 2026
    News

    FEDERAL GOVERNMENT FLAGS OFF 250-UNIT RENEWED HOPE CIVIL SERVICE ESTATE IN GWAGWALADA.

    August 19, 2026
    Add A Comment
    Leave A Reply Cancel Reply

    Latest Posts

    Governor Radda Extols Tinubu as Four Katsina Sons Clinch Federal Appointments

    April 2, 2026285 Views

    Retired Police Officers Plan “Do-or-Die” Peaceful Protest at Villa April 20

    April 5, 2026240 Views

    Emir of Katsina Approves Turbanning of Three Illustrious Sons

    April 1, 2026220 Views

    Saulawa Assumes Office as Acting Customs Provost Marshal, Promises Fair Enforcement of Discipline

    April 25, 2026164 Views

    GENERAL BABANGIDA APPLAUDS AFCSC INITIATIVE, URGES DEEPER COMMUNITY ENGAGEMENT FOR SECURITY

    May 12, 2026158 Views

    FORMER CHAIRMAN MHWUN KATSINA STATE, COMRADE MANNIR, APPEALED TO THE STATE GOVERNMENT TO FULFILLED PROMISE OF PAYING RETIRED WORKERS IN LOCAL GOVERNMENTS.

    May 12, 2026154 Views
    Stay In Touch
    • Facebook
    • YouTube
    • TikTok
    • WhatsApp
    • Twitter
    • Instagram
    © 2026 Kada Times. | Developed by ENGRMKS & CO..
    • Home
    • About Us
    • Advertise With Us
    • Privacy Policy
    • Contact Us

    Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.