Close Menu
    Facebook X (Twitter) Instagram
    KADA TIMESKADA TIMES
    • Home
    • News
    • Energy
    • Entertainment
    • Health
    • Politics
    • Religion
    • Sports
    • More
      • Business
      • Education
      • Environment
      • Opinion
      • Security
      • Traditional/tourism
    Subscribe
    KADA TIMESKADA TIMES
    Home » Taimakawa Dalibai: Shugaba Tinubu ya ba da umurnin a mayar da kuɗaɗen da EFCC ta kwato zuwa hukumar ba da tallafin karatun Dalibai,NELFUND
    Education

    Taimakawa Dalibai: Shugaba Tinubu ya ba da umurnin a mayar da kuɗaɗen da EFCC ta kwato zuwa hukumar ba da tallafin karatun Dalibai,NELFUND

    Malam Mujitaba RamalanBy Malam Mujitaba RamalanAugust 19, 20262 Mins Read
    FB IMG 1787169370457
    FB IMG 1787169370457

     

    Daga Aliyu Samba

    Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin karkatar da kuɗaɗen da Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta kwato zuwa Asusun Bayar da Lamunin Karatu na Nijeriya (NELFUND), domin ƙara ƙarfafa shirin bayar da lamunin karatu ga ɗaliban ƙasar.

    Kafar Sadarwar Sabuwar Nigeria ta ce Ministan Ilimi, Dr Tunji Alausa, ne ya bayyana hakan a ranar Laraba yayin da yake yi wa manema labarai bayani a Fadar Shugaban Ƙasa bayan kammala taron Majalisar Zartarwa ta Ƙasa (FEC).

    Ya ce Majalisar ta kuma amince da karkatar da wasu kuɗaɗen da ba a karɓa ba, ciki har da kuɗaɗen riba (dividends) da ba a karɓa ba da ke cikin kasuwanin hada hadar jari,Capital Market Trust Fund da kuma irin asusun ajiyar kudaden nan da masu su suka daina aiki da su,Dormant Account Trust Fund, zuwa shirin lamunin karatu.

    Alausa ya ce matakin na daga cikin ƙoƙarin Gwamnatin Tarayya na tabbatar da samun isassun kuɗaɗe da za su ba NELFUND damar faɗaɗa shirin da kuma tabbatar da cewa ɗaliban da ke buƙatar tallafin kuɗin karatu sun samu damar ci gaba da karatunsu.

    Ministan ya ƙara da cewa amfani da waɗannan kuɗaɗe zai taimaka wajen ƙara ɗorewar tsarin bayar da lamunin karatu, tare da rage matsalolin kuɗi da ke iya hana wasu ɗalibai ci gaba da karatu a manyan makarantu.

    Gwamnatin Tarayya ta kafa NELFUND ne domin samar da tallafin kuɗi ga ɗaliban manyan makarantu, musamman waɗanda ke fuskantar matsalar biyan kuɗaɗen karatu.

    Sabon matakin na zuwa ne yayin da gwamnati ke ci gaba da faɗaɗa shirin lamunin karatu domin ƙara yawan ɗaliban da za su iya cin gajiyarsa a faɗin Nijeriya.

    dakibai dalibai efcc kudi kudin nelfund tallafi
    Share. Facebook Twitter WhatsApp LinkedIn Email Telegram Copy Link
    Previous ArticleTinubu zai yi wa shugabannin duniya jawabi a babban Taron Majalisar Dinkin Duniya ranar 23 ga Satumba
    Next Article Ba za a cimma burin samun tattalin arzikin dala tiriliyan daya ba ,sai an sa mata cikin tsare tsaren — Shettima

    Related Posts

    Education

    Borno: Zulum Invests N15.29bn in Scholarships, Approves Fresh Support for Overseas Students

    August 19, 2026
    Education

    FUE Zaria Hosts National Conference on Food Security and Economic Development

    August 19, 2026
    Education

    Governor Inuwa Yahaya Approves N148.76m Monthly Subvention Increase for Gombe State University

    August 19, 2026
    Add A Comment
    Leave A Reply Cancel Reply

    Latest Posts

    Governor Radda Extols Tinubu as Four Katsina Sons Clinch Federal Appointments

    April 2, 2026285 Views

    Retired Police Officers Plan “Do-or-Die” Peaceful Protest at Villa April 20

    April 5, 2026240 Views

    Emir of Katsina Approves Turbanning of Three Illustrious Sons

    April 1, 2026220 Views

    Saulawa Assumes Office as Acting Customs Provost Marshal, Promises Fair Enforcement of Discipline

    April 25, 2026164 Views

    GENERAL BABANGIDA APPLAUDS AFCSC INITIATIVE, URGES DEEPER COMMUNITY ENGAGEMENT FOR SECURITY

    May 12, 2026158 Views

    FORMER CHAIRMAN MHWUN KATSINA STATE, COMRADE MANNIR, APPEALED TO THE STATE GOVERNMENT TO FULFILLED PROMISE OF PAYING RETIRED WORKERS IN LOCAL GOVERNMENTS.

    May 12, 2026154 Views
    Stay In Touch
    • Facebook
    • YouTube
    • TikTok
    • WhatsApp
    • Twitter
    • Instagram
    © 2026 Kada Times. | Developed by ENGRMKS & CO..
    • Home
    • About Us
    • Advertise With Us
    • Privacy Policy
    • Contact Us

    Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.