Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya sake jaddada aniyar Gwamnatin Tarayya ta ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro, da hukumomin gwamnati da al’ummomi domin inganta zaman lafiya, tsaro da cigaban ƙasa.
Idris ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis lokacin da Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman kan Tsaron Cikin gida, Manjo Janar Adeyinka Famadewa (mai ritaya), ya kai masa ziyarar ban-girma a Abuja.
Ministan ya tarbi ayarin , yana mai bayyana ziyarar a matsayin wata dama ta ƙara fahimtar ayyuka da nauyin da sabon Ofishin Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman kan Tsaron Cikin gida ke da shi, da kuma ƙarfafa haɗin gwiwa wajen sanar da ‘yan Nijeriya manufofi da shirye-shiryen gwamnati kan tsaro.
Ya ce: “Zaman lafiya da tsaro muhimman abubuwa ne; a haƙiƙa, su ne tubalan da duk wani cigaba zai iya ginuwa a kan su a ko’ina.”
Ya jaddada cewa ba za a iya maganin ƙalubalen tsaron Nijeriya ta hanyar matakin soji kaɗai ba, sai an ƙara haɗin gwiwa tsakanin rundunonin soji, da hukumomin tsaro, da gwamnatoci a dukkan matakai, da al’ummomi, da kafafen yaɗa labarai da sauran jama’a.
“Ba za ku iya magance wannan matsala da harbin bindiga kawai ba. Tsaro yana buƙatar haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro, rundunonin soji da sauran jama’a,” inji shi.
Ministan ya bayyana irin faɗin aikin da Hukumar Wayar da Kan Jama’a ta Ƙasa (NOA) da sauran hukumomin da ke ƙarƙashin ma’aikatar suke yi a matakin al’umma, yana mai cewa suna da muhimmiyar rawar da za su taka wajen ƙarfafa juriyar al’umma, inganta ɗaukar nauyin ɗan ƙasa da tabbatar da cewa jama’a na samun sahihan bayanai a kan lokaci.
Ya bayyana labaran ƙarya, bayanan da ba su da inganci da kuma yaɗa bayanan ƙarya da gangan a matsayin sababbin ƙalubalen tsaron ƙasa, yana mai jaddada buƙatar sadarwa mai ɗaukar nauyi da kuma ƙara wayar da kan jama’a kan kafafen yaɗa labarai da bayanai.
Tun da farko, Famadewa ya ce ya kawo ziyarar ne domin gina kyakkyawar alaƙar aiki da ma’aikatar, yana mai bayyana bayanai da wayar da kan jama’a a matsayin muhimman ginshiƙai na tsaron cikin gida na zamani.
Ya ce ofishin sa zai mayar da hankali kan haɗa bayanan sirri da sa-ido, ƙarfafa tsaron iyakokin ƙasa,da inganta gano barazanar tsaro, da kuma samar da ingantattun matakai na bayar da rahoto da mayar da martani ga rikice-rikice.
“Bayanai suna da muhimmiyar rawar da suke takawa a yaƙin da ake yi ta hanyoyin da ba na gargajiya ba. Wanda ya fara magana shi ne ke yin galaba, kuma ba za mu zauna mu ƙyale wasu su tsara mana yadda mutane za su fahimce mu ba,” inji Famadewa.
Idris ya tabbatar wa da Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawarar cewa ma’aikatar za ta ba da cikakken haɗin kai, yana mai cewa ƙarfafa haɗin gwiwa, ingantacciyar sadarwa da taka rawar gani da ‘yan ƙasa za su yi za su taimaka wajen cimma hangen Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu na ganin Nijeriya ta zama ƙasa mai ingantaccen tsaro, zaman lafiya da wadata.
Daga cikin waɗanda suka halarci taron akwai Babbar Sakataren Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Dakta Binyerem C. Ukaire; Mai Bai wa Minista Shawara na Musamman kan Harkokin Gudanarwa, Dakta Sunday Baba; Daraktan Sadarwar Jama’a da Wayar da Kai, Henshaw Ogubike; Daraktan Hulɗa da Jama’a da Ƙa’idojin Gudanarwa, Dakta Suleiman Haruna; Mai Kula da Sashen Leƙen Asiri da Nazari, Manjo Janar Emmanuel Ndagi (mai ritaya); Mai Kula da Ayyuka, Manjo Janar Hassan Dada (mai ritaya); Darakta-Janar na Hukumar Kula da Watsa Labarai ta Ƙasa (NBC), Dakta Charles Ebuebu; Darakta-Janar na Hukumar Talabijin ta Nijeriya (NTA), Dakta Salihu Abdulhamid Dembos; Darakta-Janar na Muryar Nijeriya (VON), Malam Jibrin Baba Ndace; Darakta-Janar na Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN), Malam Ali Muhammad Ali; da sauran manyan jami’ai daga Ofishin Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman kan Tsaron Cikin Ƙasa da Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai.
Sabuwar Nigeria.




