Daga Aliyu Samba
Hukumar Aikin Hajji i ta Ƙasa (NAHCON) ta sanar da kudin aikin Hajjin shekarar 2027 da Gwamnatin Tarayya ta amince da su, tare da kayyade wa jihohi ranar 2 ga watan Disamba 2026 a matsayin ranar ƙarshe ta tura dukkan kudaden Hajjin.
Hukumar ta ce an ƙayyade kudaden ne bayan tuntubar shugabannin Hukumomin Jin Daɗin Alhazai na Jihohi da masu samar da ayyukan Hajji a Ƙasar Saudiyya, tare da la’akari da farashin musayar kuɗi da kuma tsadar ayyukan da ake samarwa.
NAHCON ta bayyana cewa kudin kujerar Hajjin ya bambanta bisa yankin da alhazai za su tashi, inda alhazan yankin Maiduguri da Yola za su biya N7,560,822, yayin da na sauran jihohin yankin Arewa za su biya N7,672,822.
Alhazan yankin Kudanci kuwa za su biya N7,882,822 a matsayin kudin aikin Hajjin 2027.
Hukumar ta ce maniyyatan da suka riga suka ajiye N5,000,000 za su kammala biyan ragowar kudin domin kammala rajistarsu, yayin da sabbin maniyyata za su biya kudin ne ta hannun Hukumomin Jin Daɗin Alhazai, hukumomi ko kwamitocin jihohinsu, ko kuma bankunan da ke cikin tsarin adashin Aikin Hajji,wato Hajj Savings Scheme (HSS).
NAHCON ta kuma kayyade ranar 26 ga watan Satumba 2026 a matsayin ranar ƙarshe da za a kammala shigar da bayanan kimiyyar halittu (biometric data) na dukkan maniyyatan Hajjin 2027 a tsarin dijital na Nusuk-Masar.
Hukumar ta jaddada cewa babu wani ƙarin lokaci da za a bayar bayan wannan wa’adi, saboda tsarin daidaita bayanan maniyyata da rabon kujerun jiragen sama ya dogara ne da kammala biyan kudade da shigar da bayanai cikin lokaci.
NAHCON ta yi gargadin cewa rashin cika waɗannan wa’adodi na iya haifar da rasa kujerar Hajjin da aka ware wa maniyyata ko jihohin da abin ya shafa.
Hukumar ta ce matakin na daga cikin kokarinta na tabbatar da gaskiya, rage tsadar gudanar da aikin Hajji da kuma kare walwalar alhazan Najeriya yayin shirye-shiryen aikin Hajjin 2027.
Sabuwar Nigeria.

