Asusun Ba da Lamunin Ilimi na Najeriya (NELFUND) ya bai wa dalibai 2,152 na Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Dangote (ADUSTECH), Wudil, Jihar Kano, tallafin lamunin karatu na Naira miliyan 180.3 domin zangon karatu na 2025/2026.
Wata wasika da jami’ar ta aikewa NELFUND mai dauke da kwanan wata 13 ga Yuli, 2026, ta tabbatar da cewa kudaden sun shiga asusun jami’ar domin biyan kudin daliban da suka ci gajiyar shirin.
Takardar ta bayyana cewa an biya kudaden ne a rukuni hudu, inda rukunin K ya samu Naira miliyan 78.9 ga dalibai 946, yayin da rukunin L ya samu Naira miliyan 75.8 ga dalibai 900.
Haka kuma, rukunin M ya samu Naira miliyan 20.6 ga dalibai 247, yayin da rukunin N ya samu Naira miliyan 4.9 ga dalibai 59.
Jimillar kudaden da jami’ar ta karba ya kai Naira miliyan 180,346,256, wadanda suka shafi dalibai 2,152 a zangon karatun 2025/2026.
Jami’ar ta bayyana godiyarta ga NELFUND bisa shigar da dalibanta cikin shirin lamunin karatu, tana mai cewa tallafin zai taimaka wajen rage musu nauyin kudaden karatu da sauran bukatun ilimi.
Kafar Sadarwar Sabuwar Nigeria ta ce Shirin lamunin karatu na NELFUND na daga cikin matakan da gwamnatin Tarayya ke amfani da su wajen rage matsalolin kudi da ke hana wasu dalibai ci gaba da karatun jami’a da sauran manyan makarantun kasar.

